Select your region
and interface language
We’ll show relevant
Telegram channels and features
Region
avatar

Mohiddeen Online

MohiddeenOnline
Barka da zuwa Mohiddeen Online. Sauke app dina don karanta rubuce-rubuce da kallon videos masu amfani 👇 https://play.google.com/store/apps/details?id=com.absoft.mohiddenonline
Subscribers
1 350
24 hours
-1
30 days
1
Post views
742
ER
54,96%
Posts (30d)
Characters in post
763
Insights from AI analysis of channel posts
Channel category
EDEducation General Education News
Audience gender
Female
Audience age
25-34
Audience financial status
Middle
Audience professions
Technology & Software Development
Summary
May 30, 07:33
Media unavailable
1
Show in Telegram

🎉
GABATAR DA SABON COURSE: DATA ANALYSIS
Muna farin cikin sake muku wannan sabon course din namu mai suna “Data Analysis for Beginners.”
Data Analysis
yana koyar da yadda ake zakulo wasu muhimman bayanai a cikin data. Wannan course din yana da muhimmanci ga 'yan kasuwa, ma'aikatan asibiti, bankuna da duk wani fannin da ke hulda da bayanai - wato data.
Wannan course din na 'yan koyo ne, wato “
absolute beginners
” wadanda ba su da wani experience a kansa.
💠
WANNE AMFANI WANNAN ILIMIN ZAI MUKU BAYAN KAMMALAWA
?
✔️
Sanin yadda ake data analysis a tools din da ya dace
✔️
Koyon yadda ake data manipulation, conditional formatting da aiki da functions
✔️
Sanin yadda ake zakulo muhimman bayanai a cikin data da creating data visualization
💠
ABUBUWAN DA AKE BUKATA DON FARAWA
—Computer, ko Android, ko iPhone, ko Chromebook
Akwai 30% discount ga wadanda suka shiga wannan course din daga yanzu har zuwa gobe 07:00am.
Ke nan yanzu N2,100 kacal za ku biya har zuwa gobe da safe.
#LearnOnFlowdiary
#DataAnalysis

May 28, 19:03

YAUSHE ZA A KAWO MANA DATA ANALYSIS?
Ku shirya, a wannan satin za mu sake muku sabon course dinmu mai suna “
Data Analysis for Beginners

Data Analysis yana koyar da yadda ake zakulo wasu muhimman bayanai a cikin data. Wannan course din yana da muhimmanci ga 'yan kasuwa, ma'aikatan asibiti, bankuna da duk wani fannin da ke hulda da bayanai - wato data.
Wannan course din na 'yan koyo ne, wato “absolute beginners” wadanda ba su da wani experience a kansa.
💠
ABUBUWAN DA ZA KU KOYA A CIKI

Mene ne data analysis da matakansa

Yadda ake aiki da computer ko waya

Working with Power BI

Working with Google Sheets

Working with WPS Office

Data cleaning and preparation

Data manipulation

Conditional formatting

Data visualization
💠
WANNE AMFANI WANNAN ILIMIN ZAI MUKU BAYAN KAMMALAWA?
✔️
Sanin yadda ake data analysis a tools din da ya dace
✔️
Koyon yadda ake data manipulation, conditional formatting da aiki da functions a tools kala-kala
✔️
Sanin yadda ake zakulo muhimman bayanai a cikin data da creating data visualization
💠
ABUBUWAN DA AKE BUKATA DON FARAWA
—Kana da computer?
—Ko wayar Android ko iPhone?
—Ko computer Chromebook?
Kawai ka zo, wannan course din naku ne.
Za a sake wannan course din ranar Alhamis, 30th May 2024 in Allah Ya yarda
BUGU DA KARI...
Akwai 30% discount ga wadanda suka shiga course din a farkon 24 hours na sake shi.
KU SHIRYA, KU HANZARTA.
#LearnOnFlowdiary
#FlowdiaryApp
#Hausa
#DigitalSkills
#DataAnalysis
#NewCourse

May 18, 12:53
Media unavailable
1
Show in Telegram

A wannan makon ma muna tare da Muhammad Auwal Ahmad, CEO, Flowdiary don tattaunawa a kan maudu'in da ke sama.
Za a yi kamar haka:
Rana: Duk ranar Asabar
Wuri: Flowdiary Discussion Group (Telegram)
Lokaci: 09:00 PM
Shiga group:
https://t.me/flowdiary
#FlowdiaryApp
#LearnOnFlowdiary
#webinar

May 02, 06:11
Media unavailable
5
Show in Telegram

Malam Abdulrazak Rogo ya ce idan kana so ka fara cin moriyar
#digitalSkills
a shekarar 2026, tun yanzu ya kamata ka fara koya
#FlowdiaryApp
#LearnOnFlowdiary
#DigitalSkills
#Arewapeople
#Hausa

May 02, 06:11

Ba za ka samu gogewar da kake bukata a fannin computer a makarantun Nigeria ba.
Kuma ba Nigeria kadai ba, ko a kasashen Turai ba haka ake yi ba. Babu malamin da zai koyar da dalibai complete course a wani fanni na musamman.
To me za ka yi don ka fishshe da kanka?
Babban abun da za ka yi shi ne fadin Bature cewa “think outside the box” ta hanyar fantsama yanar gizo don koyon
#digitalSkills
.
Don share wa matasa hawaye, shi ya sa muka samar da makarantar yanar gizo ta Flowdiary wacce take koyar da digital skills da harshen Hausa cikin sauki.
A Flowdiary muna koyar da courses sama da 40 da harshen Hausa. Duk wanda ka zama ka kware a kansa zai maka amfani.
#FlowdiaryApp
#LearnOnFlowdiary
#DigitalSkills
#Hausa
#Arewapeople

April 15, 07:44
Media unavailable
1
Show in Telegram

Ranar Alhamis 18th April 2024 za mu sake muku sabon course dinmu mai suna “Cyber Security for Intermediates” in Allah Ya yarda.
Daliban Cyber Security jiran da kuke yi ya zo karshe.
Bugu da kari, za ku iya cin garabasar 50% discount har ma tsawon 24hours da sake course din.
Ku jira 18th April...
#NOTE
: Ana bukatar computer
#FlowdiaryApp
#LearnOnFlowdiary

February 13, 21:24

MENE NE FREELANCING?
TA YAYA AKE SAMUN KUDI DA SHI?
YAYA AKE YI?
💠
Amsa
👇
“Freelancing” ba komai yake nufi ba face “aikin kadago” a yanar gizo.
A garinku akwai masu aikin kadago kamar
👇
—Tela aikinsa dinki
—Lebura aikinsa dako
—Magini aikinsa gini
—Direba aikinsa tuki
—Makanike aikinsa gyaran mota
—Mai wanki da guga
—Mai gyaran wutar lantarki
—Mai fenti
—Mai gyaran waya ko janareto
—Mawaki ko makadi
—Malami, likita, ko marubuci
—Mai faskare
—Dan kwallo
—Mai shara
....da sauransu duka aikin kadago suke yi.
Duk aiki suke yi a biya su. Cikin sauki dai, aikin kadago shi ne aikin da za ka yi a biya ka.
To shi kuma FREELANCING shi ne aikin kadagon da za ka yi a yanar gizo — da wayar hannu ko computer don a biya ka.
MISALI
👇
—Web developer - mai kirkirar shafukan yanar gizo (websites)
—App developer - mai kirkirar manhajojin waya (mobile apps)
—Graphic designer - mai kirkirar designs na hotuna kamar logo, banner, flyer, invitation card
—Video Editor - mai editing ko creating videos
—Blogger mai rubuce-rubuce a shafin yanar gizo (blog)
—Social Media Manager mai kula da social media accounts irin su Facebook, Twitter, Instagram
—Email Marketer - mai tallata hajoji ta hanyar tura sakonnin email
—Webmaster - mai kula da shafin yanar gizo wato website
—Copywriter - shi ne wanda yake tsara rubutu ko script na tallace-tallace
—Social Media Marketer - wanda ya kware a tallata hajoji a social media
—UI/UX Designer - mai kirkirar creative designs na website ko app ko wani product
—Cyber Security Analyst - mai kula da tsaron na'ura, asusai, shafukan yanar gizo, ko manhajoji
—Bug Bounty Hunter - wanda yake gano kuskure a shafukan yanar gizo don kada a samu matsalar kutse
—Video Ads Creator - mai kirkirar videos na tallace-tallace
—Consultant/Tutor - malami mai koyar da karatu ko bayar da horo
—Digital Marketer - wanda yake tallata hajoji a yanar gizo
...da sauransu
Kun ga kowanne daga cikinsu yana aikinsa kuma ana biyansa.
💥
YAYA AKE SAMUN KUDI DA FREELANCING?
Aiki za ka yi a yanar gizo da wayarka ko computer a biya ka, shikenan.
💥
MATAKAN FARA FREELANCING
#1 — Ka zabi bangaren da kake so ka yi aiki, misali; bisa ga wadanda muka lissafo a sama
#2 — Ka koyi skill din wannan bangaren
#3 — Ka nuna sample na ayyukanka, wato projects din da ka yi bayan ka koyi wannan skill din. Ta haka za a san cewa za ka iya irin wannan aikin
#4 — Ka fara yi wa wasu mutane aiki da araha, ko kuma kyauta, hakan zai sa su gayyato maka mutane ka yi musu aiki
#5 — Ka nuna wa duniya aikinka ta yadda mutane za su kawo aiki ka yi musu
Wannan shi ne takaitaccen bayani game da FREELANCING.
Sai dai kuma duk batun guda daya ne, “ba za ka iya zama FREELANCER ba sai ka iya
#digitalSkills
” — abun da muka dukufa wajen koyarwa.
Zo ku koya a Flowdiary cikin sauki.
#LearnOnFlowdiary
#FlowdiaryApp

February 10, 08:47
Media unavailable
1
Show in Telegram

KOYON
#DIGITALSKILLS
BA YA BUKATAR GAGGAWA...
SABODA SHI KARATU BA SHA-YANZU-MAGANI-YANZU BA NE
—Ana bukatar mai neman ilimi ya rinka bincike, tambayar masana da mentors
—Wajibi ne dalibi ya nutsu ya koyi abun da ake yi, idan kuma bai gane ba ya yi tambaya
—Ba a zama malami, masani, ko kwararre a dare daya
—Dole ne mai neman ilimi ya daina gaggawa
—Domin cimma duk wani buri na duniya da lahira, dole sai an jure, an yi hakuri, kuma an jajirce
IDAN KA YI WADANNAN, TO KA CIMMA 60% NA LADUBBAN NEMAN ILIMI.
Allah Ya kara wa dalibanmu basira, hakuri da juriyar karatu, amin
#LearnOnFlowdiary
#FlowdiaryApp

February 09, 06:29
Media unavailable
1
Show in Telegram

Pls kowa ya je ya yi voting
👇
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=pfbid02U98RjmCY8HPtB8Q3iu8oLZHHx9DrF8m1uyox4BhUpdjaCBy7DfKH4bnf5RisccPYl&id=100064152544328&mibextid=Nif5oz

February 09, 06:29

Pls ku je ku yi voting