
AREWA STRIVERS
A farkon shekarar 2011, wani programmer mai suna Stefan Thomas ya samu kyautar Bitcoin guda 7,002 bayan ya yi wani bidiyo da ke bayanin Bitcoin a farkon lokacin sa.
Ya adana private keys ɗin a cikin IronKey USB mai tsananin tsaro. Daga baya ya manta password ɗin.
IronKey na ba ka gwadawa guda 10 kacal idan ka manta password ɗin ka kafin ya kulle kansa na har abada bazaka sake samun access dashi har abada.
Zuwa yanzu dai Stefan Thomas ya gwada password a ƙoƙarin sa na dawo da Bitcoin ɗin sa sau 8, yanzu gwadawa 2 ce kacal ce ta rage masa.
A yau waɗannan 7,002 BTC sun kai sama da kusan $500 million.
Wallet ɗin har yanzu tana kulle, yana jiran ranar da zai sake gwada waɗannan password ɗin sau biyu na ƙarshe daya rage masa ko zai dace ya tuna daidai ya buɗe Wallet ɗin.
🔐
₿
Wace shawara zaku bashi?
SABON LABARI: Pumpfun na shirin zuwa da tsarin 'multichain', a inda zasu fara bada dama a ƙirƙiri tokens akan Base, BSC, Ethereum da kuma Monad.
Wannan na nufin masu amfani za su iya ƙirƙira ko ƙaddamar da tokens a kan waɗannan blockchains daban-daban ɗin, ba a kan chain ɗaya ba na Solana da aka san su.
Matakin na iya ƙara yawan masu amfani da kuma faɗaɗa tasirin Pumpfun a cikin kasuwar crypto.
Binance ta shigar da ƙara a kotu kan Wall Street Journal bisa zargin ɓata suna.
Kamfanin ya ce rahoton da jaridar ta wallafa ya ƙunshi bayanai marasa gaskiya da suka cutar da martabar su.
Duk wanda ya fahimta da wuri, daga baya ake gane gaskiyar abin da ya faɗa. Lokaci ne kawai bai yi daidai da lokacin da mutane suke gani ba.
I wasn't wrong i was just early. GM
Wayarka ta iPhone tana magana da kai kusan kullum. Amma ka taɓa sanin muryar wace ce?
A shekarar 2005 wata mata ta shiga ɗakin recording tana karanta kalmomi marasa ma’ana domin a adana su don wani aikin fasahar magana.
Sa’o’i 4 a rana.
Kwana 5 a mako.
Tsawon watanni.
Ta yi tunanin aikin speech database ne kawai. An biya ta kuɗin studio sau ɗaya kacal saboda aikin da ta yi.
Shekara 6 bayan haka Apple ta ƙaddamar da Siri a iPhone 4S.
Duniya ta fara jin muryarta miliyoyin mutane suna amfani da ita a kullum. Amma ita kanta ba ta sani ba.
Sai bayan wani abokinta ya aiko mata da email lokacin da aka ƙaddamar da iPhone 4S. A nan ne ta gane cewa muryarta ce Siri.
Kamfanin Apple yau darajarsa ta kusa $4 trillion, amma ba a taɓa ambaton sunanta ba.
Babu royalties.
Babu wani ƙarin lada.
Ɗaya daga cikin muryoyin da aka fi sani a tarihi, amma babban kamfanin fasaha sun yi watsi da ita ba tare da ba ta wani ƙarin lada ko diyya ba.
📌
Darussa daga wannan labari:
1️⃣
Ka fahimci darajar abin da kake bayarwa kafin ka sa hannu a kowace yarjejeniya.
2️⃣
Aikin da ka yi yau na iya zama babbar fasaha gobe.
3️⃣
A duniyar tech, haƙƙin mallaka da kwangila suna da muhimmanci sosai.
4️⃣
Wani lokaci mutane sukan gina manyan abubuwa amma ba su san darajarsu ba sai bayan lokaci.
Wani lokaci muryar da duniya ke ji kullum. Ba lallai mai ita tana samun komai daga ciki ba.
🎙️
Mu kalli gida Nijeriya, Kamfanoni ko a misali na sadarwa, nawa kuke tunanin suna biyan masu ɗaura musu murya?
Idan ana biyan su da kyau kuma ana ba su haƙƙinsu, da yawancinsu sun zama millionaires a yau.
Wannan labarin ya bazu a jiya a duniyar crypto, dalilin haka aka samar da coin mai suna $SIRI akan Solana don a karrama wannan baiwar Allahn da Fees, tayi interacting da coin ɗin, dalilin haka ya buga $1 million a market cap. A dalilin haka zata amfana, suma kuma ƴan trenchers sun ƙaru. Har yanzu coin ɗin yana $325K market cap.
Labari na baku don ku fahimci yadda wani yanki na harkar Memes yake tafiya a yanzu kafin mu shiga karatu gadan-gadan.
Kwanaki da yawan mu mun samu airdrop ɗin Pengu daya faranta mana rai wasu har $1,000 zuwa sama sun samu. A kwanakin nan Pengu sunyi haɗin gwiwa da Jupiter suna bada dama ayi minting na wani NFT. NFT ɗin kyauta ne sai dai ana biyan 0.013 SOL domin minting, wanda yake kusan $1.1
Idan kana da Jupiter, kuma updated ce, kai tsaye ka je ka danna inda na zagaye a hoto na biyu kayi minting. Ƙila Jupiter ko Pengu in zasuyi wani airdrop ɗin a gaba su kalle masu NFT ɗin. Idan bai nuna maka ba, zaka iya amfani da link ɗin dana saka a ƙasa kayi pasting a Jupiter wallet ɗinka kayi claimin. Ba referral llnk bane.
Link:
sbts.pudgypenguins.com/pudgypenguins
Abin lura:
Dole ne a yi minting ɗin ta cikin Jupiter App. Bazai yiwu ta wata wallet ba.
Idan ba ka da Jupiter:
Sauke app ɗin, sannan kayi import Solana wallet ɗinka wanda ka taɓa yin swap da shi daga 27 September 2025 zuwa yanzu.
Idan kuma baka taɓa swap ba, zaka iya yin swap ɗaya kafin 20 March domin ka zama eligible.
Za'a rufe minting 3 ga watan April 2026.
Ubangiji Allah ya bamu sa'a.
LABARI MAI DUMI: Mataimakin Ministan Harkokin Waje na ƙasar Iran, Kazem Gharibabadi, ya bayyana wa gidan talabijin na ƙasar cewa wasu ƙasashe sun tuntubi Iran domin batun tsagaita wuta.
A cewarsa, ƙasashen da suka yi wannan tuntuba sun haɗa da China, Russia da kuma France.
Ana ganin wannan mataki a matsayin yunƙuri na rage rikicin da ke ƙaruwa a yankin, yayin da duniya ke ci gaba da sa ido kan halin da ake ciki.
Yau Ce Rana Ta Ƙarshe da Zanyi Magana Akan Taka
Indai kayi Taka, kuma kaga wannan post ɗin, ka saka llnk ɗinka a comment don ka samu ka cika adadin da kake so a Taka har kayi withdraw.
Idan bakayi ba, kuma kana da ra'ayi, zaka iya yi yanzu sai kaima ka saka llnk ɗinka a comment ka samu abinda ka samu. Ina yin haka ne don ku samu ku cire, kuma ku amfana In shaa Allahu.
https://os8.me/5N77WE
https://os8.me/5N77WE
Llnk ɗin ake dannawa, sai ku sauke application ɗinsu daga Playstore, kuyi face verification, sai ku saka link a comment don wasu suyi amfani dashi.
GM
An sayar da wannan lambar ta 'Anonymous Number' ta Telegram +888 8 777 akan kuɗin 651,358 TON (kimanin $882,200), wanda ya kafa sabon 'record' a matsayin lamba mafi tsada da aka taɓa sayarwa a Fragment.
Hakan na nuna yadda kasuwar Anonymous Numbers a cikin tsarin TON ke ci gaba da jan hankali da kuma samun masu zuba jari.
Ni dai duk kuɗi na bazan iya haka ba. Kai zaka iya?
Duk da cewa abinda Kabeer 2Pac yakeyi duk wani mai hankali baya goyon bayan hakan, amma idan muka kalli fuskar abin ta fuskar crypto, zaka fahimci cewa mutanen crypto musamman na Nijeriya anyi mana nisa sosai ta fuskar development a harkar nan.
Inda daga wani sashe ne a duniya, dev wanda bashi da followers ko 1k a X zaka iske ya samar da coin akan Solana da sunan Kabeer 2Pac ko wani abu daya shafi trend ɗin sa na shirmen da yakeyi, abin murna ne ma da farin ciki a samo Kabeer 2Pac yayi interacting da token ɗin ta hanyar yayi claimin fees, sai dai kaji coin ɗin idan da nasara ya buga million dollar market cap saboda yana tafiya viral sosai har a yanzu. Aƙalla idan coin ɗaya yayi running a waɗanda aka alaƙanta dashi kuma ya samu fees ɗin, zai iya samun $20k zuwa $100k a fees. Daga nan sai ya daina wannan shirmen ya kama hanyar neman ilimi da kuma ya inganta rayuwar sa ya daina yiwa kansa illa ta hanyar zuba shirmen nan a kansa.
Amma abin da zai baka mamaki, duk wannan trend ɗin da Kabeer 2Pac yakeyi a Nigeria zaiyi wahala idan ya taɓa samun N10 million. Da yawan wasu mutane da wani abu nasu yayi trending akan Solana ko BSC, wasu basu ma san menene wallets ba balle yadda ake tafiyar da tsarin, hakan kuma ya samu ne daga taimakon da devs sukeyi.
Mu anan Nigeria idan ka ɗauko tsarin ci gaba, mutane zasu nuna maka goyon baya, su nuna suna farin ciki, daga an fara samun nasara sai kowa ya alaƙanta kansa da abin don aci moriyar abin dashi, amma da an samu matsala a wani wajen, a ranar da aka samu kuskure ba kowa bane zaiyi maka uzuri ba, balle ayi tunanin tsayawa a gyara don wannan nasarar ta ɗore ba, irin yadda muke mu'amalar abu haka, ya ƙara durƙusar damu a Arewa da Nigeria baki ɗaya.